JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

An shirya taron tattaunawar masanan gida da waje na kwalejojin Confucius na shekarar 2021

发布时间:2021-12-11

       

A ranar 9 ga watan Disamba, an shirya taron tattaunawar masanan gida da waje na kwalejin Confucius na jami’ar BFSU na shekarar 2021. Taken taron shi ne ilmin koyar da Sinanci na kasa da kasa bayan cutar Covid-19, don lalubo bakin zaren warware matsalolin da ake fuskanta wajen koyar da Sinanci, bayan barkewar cutar Covid-19, da tattauna hanyoyin da za a bi wajen tinkarar kalubale, da ciyar da sha’anin koyar da Sinanci mai inganci gaba.

       Sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dinghua kuma mataimakin sakatare kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar kuma shugaban jami’ar Yang Dan da shugaban jami’ar koyon harsunan waje ta Koriya ta Kudu Hankuk Kim In Chul da shugabar jami’ar koyon harsunan waje ta Moscow ta Rasha Irina Kraeva sun halarci bikin bude taron ta hoton bidiyo. Wakilan kwalejojin Confucius na kasashen daban daban sun tattauna matakan da za a dauka wajen shirya ayyuka a Intanet da koyarwa ido da ido da kan intanet. Mambobin kwamitin gida da waje na kwalejin Confucius na BFSU da shugabannin kwalejoji da suka yi ritaya kimanin 100 sun halarci bikin.

NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC