JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

BFSU ta fara horar da masu aikin sa kai na wasannin Olympics na Beijing na 2022

发布时间:2021-11-24

A ranar 10 ga watan Nuwamba, aka kaddamar da bikin horar da masu aikin sa kai na wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing na shekarar 2022 na jami’ar BFSU. Mataimakiyar shugabar dake kula da aikin sa kai na kwamintin wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing Madam Wang Lina da mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminis ta BFSU Su Dapeng sun halarci bikin. Wakilan rukunin kula da aikin sa kai na wasannin Olympics na BFSU da malamai da dalibai kuma masu aikin sa kai 500 sun halarci bikin.

Za a shafe wata guda ana gudanar da horaswa gare su, kuma za a kunshe da fannonin 4 watau karatu, da kara ilmi, da gwajin aiki, da kyautata aiki, don daukaka ingancin aikin sa kai na malamai da dalibai na BFSU daga duk fannoni.

A yayin gasar wasannin Olympics na lokacin sanyin Beijing na shekarar 2022, jami’ar BFSU za ta tura masu aikin sa kai kimanin 800 don ba da aikin sa kai a fannonin dake shafar harshe, karbar bakunci, da tafiyar da harkokin yada labaru da dai sauransu, kuma za su yi ayyuka a duk dakunan wasannin Olympics a biranen Beijing da na Zhang Jiakou, kuma yawan dalibai masu aikin sa kai na BFSU shi ne mafiya yawa a cikin duk jami’o’in kasar Sin. A sa’i daya kuma, malamai da dalibai kimanin 100 za su bayar da aikin fasara a cibiyar ba da hidima game da fasara ta Beijing.

NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC