JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

An kaddamar da bikin cika shekaru 80 da kafuwar BFSU

发布时间:2021-10-04

A ranar 26 ga wata, an kaddamar da bikin cika shekaru 80 da kafuwar jami’ar koyon harsunan waje ta Beijing watau BFSU. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika da sakon taya murna ga tsoffin farfesoshin jami’ar, inda ya taya murnar cika shekaru 80 da kafuwar jami’ar, kana ya nuna kyakkyawar gaisuwa ga malamai da dalibai da abokan karatun jami’ar.

A yayin bikin, mataimakin ministan ilmin Sin Zhong Denghua ya yi jawabi, inda ya bayyana cewa, bayan da aka kafa jami’ar BFSU, ta horar da fitattun dalibai a jere wajen harkokin diflomasiyya, da cinikin kasashen waje, da sha’anin koyarwa ta harsunan waje, har ma harkokin tafiyar da harkokin waje. Yana fata jami’ar za ta ci gaba da kokari wajen koyarwa, don horar da fitattun kwararru dake kishin kasar Sin da sanin kasashen duniya a fannoni daban daban. Yana sa ran jami’ar za ta inganta horar da malamai, don sanya tsoffin malamai da suka ci gaba da taka rawar a zo a gani wajen taimakawa ragowar malamai, don ba da shugabancin wajen koyar da dalibai.

Mataimakin sakatare janar na M.D.D. Movses Abelian ya aika da sakon taya murna, inda ya waiwaiyi tarihin hadin gwiwa tsakanin M.D.D da jami’ar, yana fata jami’ar za ta ci gaba da ba da gudummawa wajen horar da fitattun kwararrun harsunan waje.

A madadin jami’ar, babban sakataren jam’iyyar kwaminis ta jami’ar Wang Dinghua ya jinjina wadanda suke dora muhimmanci sosai kan bunkasuwar jami’ar. Ya bayyana cewa, a cikin shekaru 80 da suka gabata, jami’ar ta tashi tsaye wajen raya sha’anin koyar da harsunan waje a kasar Sin, tana sahun gaba wajen mu’amala da yin koyi da wayewar kan kasashen duniya, kuma tana ingiza kasar Sin cikin yunkurin dunkulewar kasashen duniya. Farfesa Wang ya nanata cewa, shekarar 2021 shekara ta bude sabon shafi wajen zamanintar da kasar Sin mai ra’ayin gurguzu daga duk fannoni, kana shekara ta farko wajen cimma burin raya kasar Sin na shekaru dari-dari na biyu, za a yi amfani da damar murnar cika shekaru 80 da kafuwar jami’ar, don kokarta wajen ba da gudummawar gabatar da kasar Sin ga kasashen duniya, da kara fahimtar kasashen duniya game da kasar Sin.

Shugaban jami’ar Yang Dan ya yi jawabi, inda ya waiwaiyi tarihin jami’ar, kuma ya yi hangen gaba. Ya ce, jami’ar BFSU jami’ar da ta fi fice wajen koyar da harsunan kasashen waje. Yayin da ake shirya manyan batuttuwa ko muhimman bukukkuwa, abokan karatu na jami’ar suna tashi tsaye a ciki, don kara sanin kasar Sin game da kasashen duniya da kara sanin kasashen duniya game da kasar Sin. Farfesa Yang ya yi nuni da cewa, a sabon yanayin da ake ciki, jami’ar za ta kokarta wajen raya jami’ar dake da halayye musamman, wadda kunshe da fannoni daban daban kuma ta shahara a duk duniya, kana jami’ar za ta zama mai shugabanci wajen nazarin harsunan duniya ta fasahohin zamani, da mai jagoranci wajen yin gyare-gyare game da sha’anin koyar da harsunan kasashen duniya, da mai sahun gaba wajen kirkiro da sabbin tunani a cikin duk jami’o’in koyar da harsunan waje na kasashen duniya.

A madadin ragowar sauran jami’o’in kasar Sin, shugaban jami’ar Peking Hao Ping ya yi jawabin fatan alheri, inda ya bayyana cewa, a cikin shekaru 80 da suka gabata, jami’ar BFSU ta zama jami’ar da ke koyar da harsunan waje mafiya yawa, kuma wadda ke da kwarjini da tasirin nazari sosai a duniya.

A madadin jami’o’in da ke da hadin gwiwa da BFSU, shugaban jami’ar Lomonosov Moscow Victor Antonovich Sadovnichy ya aika da sakon taya murna ta hoton bidiyo, kuma a madadin jakadun kasashen waje a kasa Sin, jakadan Hadaddiyar Daular Larabawa Ali Obaid Al Dhaheri ya yi jawabin fatan alheri. A madadin abokan karatu, direktan majalisar wakilan jama’ar kasar Sin Zhang Yesui ya yi jawabi, yayin da shugabar kwalejin fassara na jami’ar Ren Wen ta yi jawabi a madadin malaman jami’ar.

Zaunannen mataimakin babban sakataren kwamintin kula da harkokin ilmi na brinin Beijing Zheng Jichun, da tsohon ministan harkokin wajen kasar Sin Li Zhaoxing, da mataimakiyar direktan kwamitin kula da Sinawa a kasashen waje, da batutuwan Hongkong da Macau na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Qiu Yuanping, da Manjo janar na rundunar ‘yan sandar kasar Sin kuma mataimakin kwamishina mai kula da harkokin siyasa Chen Jianfeida sauran manyan baki a fannonin diflomasiyya da cinikin waje da sha’anin koyar da harsunan waje da tafiyar da harkokin waje na kasar Sin sun halarci bikin.


NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC