JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

An kaddamar da bikin fara karatu na shekarar 2021 a BFSU

发布时间:2021-09-19

A ranar 7 ga watan Satumba, an kaddamar da bikin fara karatu na shekarar 2021 a jami’ar BFSU. Dalibai masu neman digiri na farko da na biyu da na uku da daliban kasashen waje kimanin 3400 za su fara karatu a jami’ar. Tsohon mataimakin sakatare janar na M.D.D kuma manzon musamman na gwamnatin Sin game da harkokin Turai, kuma abokin karatu na kwalejin Turanci na shekarar 1973 Mista Wu Hongbo da babban sakatare janar na jam’iyyar kwaminis ta jami’ar BFSU Wang Dinghua, da mataimakin sakatare janar kuma shugaban jami’ar Yang Dan, da mataimakin sakatare janar kuma mataimakin shugaban jami’ar Jia Wenjian, da zaunannen mamban jam’iyyar kuma maimakin shugaban Sun Youzhong, da mataimakin sakatare janar kuma sakatare janar da ke kula da harkokin ladabtarwa Hu Zhigang, da mataimakin sakataren janar Su Dapeng, da zaunannun mambobin jam’iyyar kuma mataimakan shugaban Ding Hao da Zhao Gang sun halarci bikin. Shugaba Yang Dan ya yi maraba da zuwan sabbin dalibai na shekarar 2021, inda ya yi jawabi mai take “Koyon harsunan waje da samun bunkasuwa daga duk fannoni don ba da gudummawa ga raya kasashen duniya.”


NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC