JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

BFSU ta fidda sabon littafi game da lissafan shekarar 2021

发布时间:2021-09-19

A ranar 3 ga watan Satumba, an kaddamar da bikin fitar da sabon littafi game da lissafai da ma’aunan kasashen duniya na shekarar 2021 a kamfanin dab’in dake kula da harkokin koyarwa da nazarin harsunan waje. Shugaban jami’ar BFSU kuma mataimakin sakatare janar na jam’iyyar kwaminisanci ta jami’ar, Yang Dan ya shugabanci tawaga don gudanar da aikin nazarin kasashen duniya bisa lissafai. Wadannan lissafai sun kunshe da lissafin nazarin kungiyoyin kasa da kasa, lissafin kwarewar Sin wajen harsunan waje, da lissafin kirkiro da sabbin tunani da fasahohin duniya, da lissafin tasirin jami’o’in kasashen duniya, da lissafin ingancin sadarwa na akanta, da lissafi game da yadda aka dunkulewar kasar Sin a kasashen duniya. Wannan shi ne karo na farko da aka fidda wadannan lissafai a duniya. A gun bikin bude cibiyar nazarin aikin fasara na Sin da aka yi a jami’ar BFSU a watan Mayu na bana, an riga an bayar da lissafin kwarewar Sin game da fasara da lissafin kwarewar jami’o’in Sin wajen fasara.


NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC