Daga ranar 20 ga watan Yuli zuwa ranar 7 ga watan Agusta, jami’ar koyon harsunan wajen Beijing watau BFSU ta shirya bukukkuwan koyon Sinanci na lokacin hutu na zafi na Immersion and Impression ga daliban sakadaren Turai, da kwas don samun fahimtar yankin kudancin kasar Sin har da kwas ga daliban jami’o’i.
Wadannan ayyukan mu’amala da aka shirya a kan shafin Internet sun dora muhimmanci kan koyon Sinanci da kara samun fahimtar al’adun kasar Sin. An ba da lecca da koyar da darussa da dama, har ma an koyar da wasu darussa kai tsaye, don taimakawa dalibai don kara sanin kasar Sin ta zamani daga duk fannoni, kana da kyautata kwarewarsu wajen koyon Sinanci.
An ba da lecca game da harshen Sinanci, da ziyara a birnin Beijing, da koyar da harshen Sinanci da harsuna daban daban da dai makamantansu, dalibai 176 da suka fito daga kasashe 11 na Rasha, Hungariya, Bulgariya, Czech, da Spaniya sun halarci wadannan darussa.
Game da ayyukan koyon Sinanci don kara fahimtar yankin kudancin kasar Sin da aka shirya su da harsunan Sinanci da Jamusanci, an dora muhimmanci a kan kara fahimtar dalibai game da bunkasuwar wannan yanki, dalibai 97 da suka fito daga kasashe 14 na Jamus, Luxemburg, Portugul, Birtaniya da Poland sun halarci wannan kwas.