JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

An fara darasin kasa da kasa na ilmin Confucius da al’adun kasar Sin na 2021

发布时间:2021-08-05

A ranar 20 ga wata, an kaddamar da bikin bude kwas na kasa da kasa na ilmin Confucius da al’adun kasar Sin na shekarar 2021 da hadadden kwamitin nazarin Confucius na kasa da kasa da jami’ar koyon harsunan wajen Beijing BFSU suka shirya. Sakataren janar na kwamintin Confucius Jia Deyong da zaunannen mamban jam’iyyar kwaminis ta BFSU kuma mataimakin shugaban jami’ar Zhao Gang sun halarci bikin.

Za a shafe kwanaki 13 ana koyo a wannan kwas, kuma za a koyar da ilmi da harsunan Sinanci da Turanci a kan Intanet. Malaman gida da waje za su koyar da dalibai sama da 120 da suka fito daga kasashe 26. A yayin bikin kaddamar da kwas, kwararru da masana da dalibai da suka fito daga jami’o’in Peking da Tsinhua da BFSU da Oxford da Munich da Australiya sun halarci bikin bude kwas.


NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC