A ranar 2 ga watan Yuli, an gudanar da bikin kammalawar karatu na daliban jami’ar BFSU na shekarar 2021.
A bana, dalibai 61 sun samu digiri na uku, yayin da dalibai guda 1064 sun samu digiri na biyu, haka kuma yawan dalibai da suka samu digiri na farko ya kai 2197. A ranar da aka gudanar da bikin, an gudanar da bukukuwa guda 7 don mika takardun digiri da digirgiri ga dalaibai. Babban sakatare na jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dinghua da shugaban jami’ar Yang Dan sun halarci wadannan bukukkuwa, gami da mika takardun digiri da digirgiri ga dalibai na kwalejoji daban daban.