A yammacin ranar 4 ga watan Disamba, shugaban kasar Salvador Nayib Bukele ya ziyarci BFSU, inda aka karrama masa da digiri na uku kuma ya yi jawabi a wajen. An yi bikin karramawa digiri na uku ga shugaban da kuma bikin gabatar da jawabi a dakin taron kasa da kasa a cibiyar nazarin Larabci ta jami’ar.
Shugaban kasar Salvador Bukele da uwargidansa Gabriela Rodríguez, da ministar tattalin arzikin kasar María Luisa Hayem da ministan kula da aikin gona da kiwon dabbobin Pablo Anliker da ministar kula da yawon shakatawa Morena Valdez da mataimakin direktan sashen kula da Latin Amurka na ma’aikatar kula da harkokin wajen Sin Lan Hu da shugaban BFSU Yang Dan da mataimakinsa Yan Guohua sun halarci bikin, kuma Mr. Yan ya shugabanci bikin.
Shugaban Yang Dan ya yi jawabin maraba da baki, a madadin sakataren jami'ar Wang Dinghua da daukancin malamai da dalibai, ya yi lale marhabin da zuwan shugaban Bukele da mika godiya gare shi. Ya yi nuni da cewa, zuwan shugaban Bukele a Sin ya nuna dankon zumuncin dake tsakanin jama’ar kasashen Salvador da Sin, kuma ya zama abun shaida ga mu’amalar al’adu da jama’a da kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu. Yana fatan zuwan shugaban a kasar Sin, zai nuna wa jama’ar Salvador game da halin maraba da baki na jama’ar Sin, kuma yana sa ran kasashe biyu za su inganta hadin gwiwa a fannoni da dama, don kara kawo alheri ga jama’ar kasashen biyu.
Yang Dan ya waiwaiyi tarihin BFSU da nasarorin da jami’ar ta samu, inda ya nanata bunkasuwar fannin karatu na harshen Spain a jami’ar. Ya bayyana cewa, zuwan shugaban Bukele a BFSU da karrama masa digiri na uku ya zama abin alfahari na BFSU. Yang Dan ya mika goron gayyata ga Bukele don ya dinga dawowa jami’ar a matsayin abokin karatu na BFSU, da inganta mu’amala a tsakanin BFSU da kasar Salvador, da raya cibiyar nazarin Latin Amurka na BFSU, don bude wani sabon shafi na dankon zumunci dake tsakanin kasashen biyu.
Yan Guohua ya karanta shawarar kwamintin kula da digiri na majalisar gudanarwar Sin ta yanka game da karramawa shugaban Bukele da digiri na uku. Shugaban Yang Dan ya mika masa da takarda.
Daga bisani kuma, Bukele ya yi muhimmin jawabi, inda ya gabatar da kasar Salvador da halayyen musamman na kabilu da matsayin musamman na wurin. Ya bayyana cewa, Salvador da Sin sun fuskanci juna ta tekun Fasific, kasashen biyu na da jama’a masu kokarta da jaruntaka, gwamnatocin kasashen biyu sun samu goyon baya sosai daga jama’a, yana fatan kasar Sin za ta kara mu’amala da kasashen Latin Amurka ta kasar Salvador. Bukele ya jinjina gudummawar da Sin ta bayar a yanayin dunkulewar kasashen duniya, yana ganin cewa, a halin da ake ciki yanzu, an shiga yanayi na bayan dunkulewar kasashen duniya baki daya, an karfafa mu’amala da kasashen duniya sosai, amma a sa’i daya kuma, an fuskanci matsalar rarar kayayyakin masana’antu a duniya, ya kamata kasashen duniya su kawar da nuna bambancin ra’ayi, da inganta hadin gwiwa ta bangarorin daban daban don kawar da talauci da rashin daidaito. Dole ne ko wane mutum ya dauki alhakin da ke wuyansa, don kokarta wajen kawar da talauci da yunwa a kasashen duniya. Yana fata kasashen biyu za su inganta hadin gwiwa a tsakaninsu a karkashin yanayi na bayan dunkulewar kasashen duniya baki daya, don kara yaukaka dangantakar kasashen biyu.
Bayan da ya yi jawabi, shugaban BFSU Yang Dan ya mika rubuce-rubuce na dalibi mai koyon harshen Spain na BFSU Shi Wen ga shugaban mai take ‘Sada zumunta tsakanin Sin da Salvador, don kama hanyar yadda ya kamata’. Yana sa rai za a kara kyautata dankon zumuncin kasashen biyu.
Mambobin tawagar Salvador da wakilan malamai da dalibai na BFSU da daliban Salvador a kasar Sin sama da 300 sun halarci bikin.