Daga ranar 10 zuwa ranar 18 ga watan Oktoba, sakataren jami’ar BFSU Wang Dinghua ya shugabanci tawaga don ziyartar kasashen Rasha, Finland da Holland, inda ya yi mu’amala da jami’ar koyon harsuna ta Moscow da jami’ar Herzen da cibiyar nazarin litattafan kasashen gabashin duniya ta Saint Petersburge ta Rasha, da jami’ar Tampere da ta Lapland ta kasar Finland da kungiyar nazarin harsuna ta Holland da jami’ar Leiden, inda ya daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa da dama da wadannan jami’o’i da hukumomi, kana a yayin ziyarar, ya ziyarci ofishin jakadancin dake kasashen Rasha da Finland da Holland.