A ranar 28 ga watan Yuni, BFSU ta shirya bikin kammala karatu da ba da digiri na farko ga dalibai na shekarar 2018. A bana, dalibai kimanin 1372 da suka fito daga gida da waje sun kammala karatu, inda dalibai 60 sun samu lambobin yabo na nagartattun dalibai na birnin Beijing, kana dalibai 121 sun zama fitattun dalibai na jami’ar.