Kwanan baya, ma’aikatar kula da ilmi ta Sin ta amince da kafa fannin karatu don neman digiri na farko na diplomasiyya tsakanin BFSU da jami’ar Keele, kuma an yi shirin daukar dalibai a wannan shekara. Wannan shi ne karo na farko da jami’armu ta kafa fannin karatu cikin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen waje, kuma shi ne fannin karatun diplomasiyya na farko da aka kafa a kasar Sin.