JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

Shugaban BFSU ya halarci taro karo na 4 na mu’amalar al’adu tsakanin kasashen Sin da Faransa

发布时间:2019-05-15

A safiyar ranar 24 ga watan Nuwamba, an yi taro karo na 4 na mu’amalar al’adu tsakanin kasashen Sin da Faransa a nan birnin Beijing. Mataimakiyar firaministan kasar Sin Liu Yandong da ministan harkokin wajen kasar Faransa Jean-Yves Le Drian sun shugabanci taron gami da halartar wasu bukukuwa, Shugaban jami’ar BFSU Peng Long ya halarci taron da bikin mika lambobin yabo na gasar yin jawabi da Faransanci da gidan talebijin CGTN ya shirya.

A yayin taron, Madam Liu da Le Drian sun rattaba hannu game da hadaddiyar sanarwa, inda suka ganewa idanunsu daddale yarjejeniyoyi 7 game da mu’amalar al’adu tsakaninsu, cikinsu har da yarjejeniyar dake tsakanin hedkwatar kwalejin Confucius na Sin da kwalejin kasuwanci na ESCP na Turai a kasar Faransa, bisa yarjeniyar, jami’ar BFSU za ta shirya kwalejin Confucius na kasuwanci na ESCP na kasashen Turai.

A gun bikin mika lambobin yabo na gasar yin jawabi da Faransanci da gidan talebijin CGTN ya shirya a yayin taron, Liu Yandong da Le Drian sun mika lambobin yabo ga zakaran wannan gasar wato dalibar jami’armu ta shekarar 2015 Zhang Bisi. A matsayin wani babban jigo cikin taron, gasar yin jawabi da Faransanci ta zama wata babbar gasar da aka shirya don fidda Sinawa wadanda suka lakanci da harshen Faransanci, da sa kaimi ga kara dankon zumunci da mu’amala tsakanin kasar Sin da kasashe da yankunan da ke amfani da harshen Faransanci. Ban da Zhang Bisi kuma, Zhang Shuwen wato dalibar da ta zo karatu a jami’armu a shekarar 2016 ta samu lambar yabo ta biyar, kuma Ma Fangtong wadda ke karatun digirgiri tun daga shekarar 2015, ta samu lambar yabo na 8.

NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC