A ranar 21 ga watan Satumba, ma’aikatar kula da ilmi da ma’aikatar kula da harkokin kudi da kwamitin kula da gyare-gyare da raya kasa na Sin sun fidda sanarwar jerin sunayen jami’o’in da kyawawan fannonin karatu da kasar Sin za ta kokarta don raya su, ta yadda za a habaka su har sun zama na gaba-gaba dai a duniya. A cikin sanarwar, jami’ar BFSU ta shiga cikinsu, kuma gwamnatin Sin za ta hobbasa don raya fannonin karatun jami’ar.
A cikin jerin sunayen jami’o’in Sin da kasar za ta kokarta don raya su, an hada da kyawawan jami’o’i 42, da jami’o’in wadanda suke da fitattun fannonin karatu 95, BFSU ta kasance daya daga cikinsu.