A ranar 28 ga watan Yuni, an shirya bikin kammala katatun digiri na farko na shekarar 2017 a BFSU. A wannan shekara, akwai dalibai kimanin 1302 da suka kammala karatun digiri na farko, kuma wasu 95 daga cikinsu sun samu karramawar nagartattun dalibai na birnin Beijing, kana, akwai dalibai 196 da suka samu irin yabo na nagartattun dalibai na BFSU, kazalika, dalibai kimanin 84 sun zama mambobin kula da kwamitin kungiyar abokan dalibai na BFSU.