JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

An kafa kawacen jami’o’in harsunan waje na duniya a BFSU

发布时间:2019-05-15

全球外语大学联盟配图A ranar 19 ga watan Mayu, an yi taron tattaunawa kan nazarin shiyya-shiyya da daidaita lamuran duniya kuma taron tattaunawa tsakanin kawacen jami’o’in harsunan waje na duniya. Jami’ar BFSU ta shirya kafa wannan kawace, kuma jami’o’i 30 na kasashe 16 na duniya sun zama mambobin farko a cikin wannan kawacen. Mataimakin ministan harkokin ilmin Sin Tian Xuejun da babban sakataren jami’ar BFSU Han Zhen da shugaban jami’ar Peng Long sun halarci taron.

An kafa wannan kawace bisa irin halayyen musamman na jami’o’i wajen nazarin shiyya-shiyya da kasashe daban daban, kuma wannan kawace zai bi akidar hadin gwiwa da amincewar juna, da samun moriyar juna tare, don kafa wani dandalin hadin gwiwa kan ilmi, bisa karfin nazarin harsunan waje da koyar da su, da nazarin shiyya-shiyya da kasashen daban daban, don inganta mu’amalar jama’a tsakaninsu.

An kafa kwamitin kawacen kuma shugaban jami’ar BFSU Peng Long zai zama shugaban kawacen, sauran shugaban jami’o’i za su zama mambobin kwamitin, kuma an kafa ofishin sakatariyar kwamitin a BFSU. Za a yi wani taron tattaunawa a ko wadannan shekaru biyu-biyu, don tattauna batun tunanin inganta jami’o’i, da hanyar samun bunkasuwa da horar da kwararru, da inganta fannin karatu da dai sauransu, don tabbatar da ayyukan hadin gwiwa da daddale yarjejeniyoyi.

A yayin taron, wakilan mambobin kawacen, sun daddale yarjejeniyar hadin gwiwa, don shaida kafa wannan kawace a hukunce.

Mambobin kawacen jami’o’in harsunan waje na duniya sun hada da jami’ar harsunan Azerbaijan, da jami’ar Sofia ta Bulgariya, da jami’ar Lima ta Peru, da kwalejin nazarin harsunan waje na biyu na Beijing, da jami’ar koyon harsunan waje ta Beijing, da jami’ar nazarin harsuna ta Beijing, da kwalejin nazarin tafinta na Munich,da jami’ar koyon harsunan waje ta Dalian, da jami’ar koyon harsunan waje ta Tokyo, da jami’ar koyon ilmin tattalin arziki da cinikin kasashen waje ta Sin, da jami’ar koyon ilmin harsunan waje da cinikayya ta Guangzhou, da kwalejin nazarin dangantakar kasa da kasa na Sin, da jami’ar Al Farabi ta kasar Kazakhstan, da jami’ar koyon harsunan waje ta Koriya ta Kudu, da kwalejin nazarin dangantakar kasa da kasa na Moscow, da jami’ar koyon harsunan waje ta Moscow, da jami’ar kasar Mexico da jami’ar Muhammed ta Morocco ta biyar, da jami’ar koyon ilmin tattalin arziki da cinikin kasashen waje ta Shanghai, da jami’ar koyon harsunan waje ta Shanghai, da jami’ar koyon harsunan waje ta Sichuan, da jami’ar koyon harsunan waje ta Tianjin, da kwalejin nazarin ilmin diplomasiyya na Sin, da jami’ar nazarin harsunan kasashen duniya ta Uzbekistan,da jami’ar koyon harsuna ta Kivu ta kasar Ukraine, da jami’ar koyon harsunan waje ta Xian, da jami’ar Gujarat ta tsakiya ta kasar India, da jami’ar Yogyakartata kasar Indonesiya, da kwalejin koyon harsunan waje na Zhejiang, da jami’ar Católica de Valparaíso ta Chile.

NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC