A ranar 8 ga watan Nuwamba, mataimakin firaminista kuma ministan harkokin wajen ƙasar Ireland Michael Martin ya ziyarci BFSU, inda ya yi jawabi game da alaƙar dake tsakanin Sin da Ireland da manufar diflomasiyya ta ƙasar, kuma ya yi mu’amala da malamai da ɗalibai na gida da waje. Babban sakataren kwamintin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dinghua ya halarci biki game da yin jawabi.