JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

Ministan harkokin wajen Japan ya ziyarci BFSU

发布时间:2019-05-15

A ranar 13 ga watan Afrilu da yamma, ministan harkokin wajen Japan Taro Kono ya ziyarci BFSU, inda ya yi mu’amala da dalibai da malaman cibiyar nazarin Japan ta kasar Sin. Babban sakataren kwamintin tsakiya na jami’ar Wang Dinghua da mataimakin shugaban jami’ar Jia Dezhong sun gana da shi.

Wang Dinghua ya yi maraba da zuwan ministan, inda ya yi nuni da cewa, mu’amalar da ke tsakanin kasashen biyu ta shiga wani sabon mataki a cikin tarihi, a watan Yuni na bana, za a yi taron koli na G20 a birnin Osaka na kasar Japan, shawarwarin da za a yi tsakanin kasashen biyu za su yaukaka dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu. Ziyarar ministan Kono a jami’ar BFSU, tana da ma’anar musamman ga sha’anin mu’amala tsakanin kasashen Sin da Japan da nazarin kasar Japan a jami’ar BFSU. A cikin ‘yan shekarun nan, BFSU ta kara inganta horar da dalibai, ta kara hadin gwiwa da kasashen duniya, cikinsu har da shahararrun jami’o’i da yawa na Japan.

Cibiyar nazarin Japan ta BFSU ita ce cibiyar da ma’aikatar kula da ilmin Sin da asusun kula da mu’amalar kasa da kasa na Japan suka shirya tare, ita ce hukumar nazarin Japan kawai da gwamnatin Japan ta kafa a kasashen waje, wadda za ta horar da dalibai masu digirgiri. Bayan da aka kafa ta har na tsawon shekaru sama da 30, a karkashin taimakon gwamnatocin kasashen Sin da Japan, an horar da dalibai masu digiri na biyu da na uku da malamai masu nazarin Japan da koyar da Japananci 1421, kuma ta zama abin misali wajen mu’amala da hadin gwiwar al’adu da mutane a tsakanin kasashen biyu.BFSU za ta ci gaba da inganta hadin gwiwa da jami’o’in kasar Japan.

Ministan Kono ya jinjina wa jami’ar BFSU, inda ya ce, bana zagayowar shekara ta 70 da aka kafa jamhuriyar jama’ar kasar Sin, a ko ina ana ganin farin cikin jama’ar kasae Sin da ma manyan canje-canje a kasar, idan aka kwatanta da zuwansa kasar Sin na farko wato shekaru 40 da suka gabata, an samu manyan sauye-sauye. A cikin jawabinsa, ya tabo maganar batun dalibtarsa a kasar Sin, kuma yana fatan inganta hadin gwiwa cikin aminci a tsakanin matasa, don sa kaimi ga fahimtar juna na kasashen biyu, yana sa ran cibiyar nazari za ta kara horar da kwararrun da za su taimakawa sha’anin raya dangantakar kasashen biyu.

Daga bisani, ministan Kono ya tattauna da dalibai masu digiri na biyu da na uku 10 ba na cibiyar. Dalibai sun gaya wa ministan game da fannonin nazarinsu da shirin ayyukansu na nan gaba. Ministan Kono ya karfafa zukatan dalibai da su kara kokarin karatu, da jaddada ma’anar musamman ta yin shawarwari kece da keke game da inganta fahimtar juna a tsakaninsu.

A yayin ziyarar, babban sakatare Wang Dinghua da mataimakin shugaban BFSU Jia Dezhong sun raka ministan zuwa laburaren cibiyar da dakin aikin tafinta da bikin nune-nunen hotunan kulla dangantakar diflomasiyya na shekaru 40-mu’amala da hadin gwiwa tsakanin Sin da Japan.

NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC