JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

Shugaban jami’ar nazarin harsuna ta Munich ta Jamus ya ziyarci BFSU

发布时间:2019-05-15

A safiyar ranar 16 ga watan Nuwanba, shugaban jami’ar nazain harsuna ta Munich ta Jamus Felix Mayer ya ziyarci BFSU, inda ya gana da shugaban jami’ar Peng Long, kuma shugaban Peng ya mika takardar nada shi a matsayin Furfesa don ba da lecca a lokaci-lokaci a jami’ar.

Peng Long ya jinjina goyon baya da jami’ar nazarin harsuna ta Munich ta yi, kuma ya yaba wa shirin digirgiri na tafinta da jami’o’in biyu suka yi, kuma yana fatan bangarorin biyu za su karfafa hadin gwiwa wajen fasara da nazarin kasar Jamus, kana da inganta hadin gwiwarsu wajen siyasa, tattalin arziki da dangantakar kasa da kasa.

A nasa bangare kuwa, Mayer ya yaba wa kokarin ba da lecca da jami’ar BFSU ta bayar, kuma ya more nasarorin da aka samu wajen fasarar kirkiri-kirkiri, kuma yana fatan bangarorin biyu za su kara inganta hadin gwiwa wajen horar da malamai da dalibai, da nazarin koyarwa da kafa kwalejin confucius.

NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC