JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

Firaministan kasar Netherlands Mark Rutte ya ziyarci BFSU

发布时间:2019-05-15

A yammacin ranar 12 ga watan Afrilu, firaministan kasar Netherlands Mark Rutte ya ziyarci jami’ar BFSU. Jakadan kasar Netherlands a kasar Sin Everardus Kronenburg da babban sakataren fadar gwamnati Paul Huijts, da ministan kula da harkokin waje da tsaro David van Weel, da direktan kula das ashen Asiya na ma’aikatar DAO BZ sun raka shi zuwa.

A gun bikin maraba da Mark Rutte da aka yi a laburare, jakadan Sin a kasar Netherlands Wu Ken ya halarci bikin, kuma mataimakin shugaban BFSU Yan Guohua ya shugabanci bikin.

Peng Long ya jinjina da maraba da firaministan da ya yi tattaki a jami’ar yayin da yake ziyara a kasar Sin, kuma ya gabatar da jami’ar BFSU gare su, musamman ma yanayin da ake ciki wajen raya harshen Dutch. Ya yi nuni da cewa, fannin karatu na Dutch na BFSU ba ma kawai ya kasance wani dandalin horar da dalibai masu koyon harshe ba, har ma ya zama wani babban tushe wajen nazarin kasar Netherlands da yada al’adunta.

Firaministan Rutte ya yaba wa daliban Sin wajen koyon harshen Dutch da nasarorin da suka samu, har da gudummawar da BFSU ta bayar wajen horar da dalibai masu jin harshen Dutch da yada al’adun kasar. Rutte ya gamsu da dangantakar da ke tsakanin Sin da Netherlands, kuma ya jaddada nasarorin da ya samu ta wannan ziyara, yana fata kasar Sin za ta taka muhimmiyar rawa a duniyar da take sauyawa yanzu.

Haka kuma, ya gane ma idanunsa, yadda shugaban BFSU Peng Long da jakadan Everardus Kronenburg suka bude cibiyar nazarin kasar Netherlands a jami’ar.

Ban da wannan kuma, Rutte da dalibai masu koyon Dutch da daliban kasar Netherlands a kasar Sin sun yi mu’amala, inda suka tattauna batutuwan al’adu da ilmi da tattalin arziki, da dangantakar kasa da kasa, ya amsa duk tambayoyin da daliban Sin da Netherlands suka yi masa cikin tsanaki. Yayin da aka tabo batun ilmi, ya bayyana cewa, ko da yake, an sha bamban game da salon koyar wa dalibai a kasashen biyu, amma dukkansu sun dukufa ka’in da na’in wajen koyarwa da lalubo bakin zaren warware batutuwan duniya.

Kafin aka yi bikin, dalibai masu koyon Dutch sun raya Rutte yawo a cikin BFSU da keke, kuma sun ziyarci wurin lambun sada zumunci tsakanin kasar Sin da kasashen Turai.

NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC