JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

Shugaban SOAS ya ziyarci BFSU

发布时间:2024-03-15

A ranar 12 ga watan Maris, shugaban kwalejin nazarin Asiya da Afirka na jami’ar London Adam Habib ya ziyarci BFSU. Babban sakataren kwamintin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dinghua da mataimakinsa kuma mataimakin shugaban BFSU Jia Wenjian ya gana da shi.

Wang ya bayyana halin da BFSU take biki wajen raya fannonin karatu da ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashen duniya, yana fata jami’o’i biyu za su inganta haɗin gwiwa a wajen horar da ɗalibai tare da nazarin tare don raya jami’o’i biyu.

Habib ya bayyana halin da ake ciki a SOAS, kuma ya bayyana anniyarsu ta ƙarfafa haɗin gwiwa da BFSU a fannin koyarwa da nazari tare, don lalubo bakin zaren horar da ɗalibai da samun bunƙasuwa tare.

Daga bisani kuma, Wang da Habib sun daddale yarjejeniyar haɗin gwiwa a fannin digiri na biyu.


NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC