A ranar 6 ga watan Janairu, an ƙaddamar da taron tattaunawar diflomasiytar jama’a ta sabuwar shekarar 2024 da BFSU ta shirya.Wakilan ma’aikatar harkokin wajen Sin, da ma’aikatar kula da kasuwanci, da sashen kula da tuntuɓawar ƙasashen waje, da kwamintin sada zumunci, da cibiyar nazarin da samun bunƙasuwar majalisar gudanarwar Sin, da kwamitin nazarin Turai na Sin, da tawagar ƙungiyar EU a Sin, da kwamitin kasuwancin ƙungiyar EU a Sin, da sauran jami’o’i, da cibiyoyin nazari, da kafofin yada labaru sun halarci taro. Shugaban BFSU kuma mataimakin zaunannen mamban kwamintin jam’iyyar kwaminisanci Yang Dan ya halarci bikin gami da yin jawabi.
A yayin taron, an buɗe cibiyar nazarin ƙungiyar EU da shiyya-shiyya na BFSU, da sanar da mashawarta.
A yayin taron, an kafa tarurruka masu take 2, waɗanda suka haɗa da nazarin Turai, da shawarwari da haɗin gwiwa tsakanin Sin da Turai a ƙarkashin yanayin da ake ciki yanzu. Ƙwararru da masana da suka fito daga jami’o’in da sassan nazari sun halarci taron.
A ƙarshe dai, BFSU da kwamintin kula da sadar zumuncn Sin sun shirya taron tattaunawar diflomasiyyar Sin da Turai dake da take “Sa kaimi ga fahimtar juna don kawar da saɓanin dake tsakaninsu. Wakilai a fannonin siyasa, da karatu, da kasuwanci na ɓangarorin biyu na Sin da Turai za su tattauna a ƙarƙashin taken da aka shirya da more fasahohin da ake samu don cimma matsaya.