A ranar 9 ga watan Afrilu, a cibiyar nazarin ilmin Tibet ta Beijing, aka fitar da sabon ƙamus na nazarin zamantakewa da kimiyya da fasaha na Sinanci da Turanci da harshen Tibet, kuma BFSU da kamfanin ɗab’in CP sun shirya biki tare.
Babban ƙamus na nazarin kimiyya da fasaha da zamantakewa na harsunan Sinanci da Turanci da harshen Tibet da shugaban BFSU kuma mataimakin sakatare janar na kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar Yang Dan ya tsara, inda ya shugabanci ƙwararru da masana na jami’ar Tibet da BFSU da jami’ar nazarin tattalin arziki da kuɗi na yankin kudu maso yammacin Sin, kuma ya kasance wani babban aikin nazarin kimiyya da fasaha da zamantakewar jihar Tibet. Wannan karo na farko da aka fitar da ƙamus da ke da harsuna uku don nazarin kimiyya da fasaha da zamantakewar al’umma, inda karo na farko ne akwai kalmomin da suka shafi ilmin harshe, da na fasaha, da binciken archaeology da aka fassara su zuwa harshen Tibet, wannan tana da ma’anar musamman sosai, kuma ya ƙunshe da babi 21, kuma ya haɗa da kalmomi fiye da dubu 45.