A ranar 18 ga watan Maris, an gudanar da taron ƙara-wa-juna gani game da raya ma’adanar bayanai wajen nazarin ƙasashe duniya da shiyya-shiyya na ƙasar Sin, inda ƙawacen gamayyar nazarin shiyya-shiyya da ƙasashen duniyar Sin ya shiya wannan taro a BFSU. Shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin BFSU Yang Dan ya halarci taron.
A yayin taron, ƙwararru da masana da suka fito daga jami’o’i 34 suka halarci taron, ciki har da jami’o’in Peking da Renmin da sauransu. Mahalartar taron sun tattauna sosai game da shirin kafa ma’adanar bayanan nazarin shiyya-shiyya da ƙasashen duniya daban daban, da hanyoyin da za a bi wajen gudanar da aiki.