A ranar 1 ga watan Maris, mataimakin sashen kula da tuntuɓawar waje na kwamitin shirya gasar wasannin motsa jikin Asiya Xu Jianfeng ya ziyarci BFSU, inda zaunannen mamban kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’a kuma mataimakin shugaban jami’ar Jia Dezhong ya gana da shi, inda suka yi musanyar ra’ayi game da kafa hukumar ba da hidimomin fasara da tafinta ta harsuna da yawa a lokacin wasanni.
Bangarorin biyu sun yi shawarwari game da halin da ake ciki wajen tafiyar da harkokin ba da hidimomi ta harsuna da yawa da ɗaukar masu aikin sa kai da ba da tabbaci ga tafiyar da harkoki da sauransu.
Bayan taron, Xu Jianfeng ya ziyarci cibiyar da ɗakin nune-nunen harsunan duniyar BFSU.