A ranar 24 ga watan Febrairu, a yayin taron odar littattafan Beijing karo na 35 da aka shirya a birnin Beijing, an shirya taron manema labaru game da sabbin sakamakon fasarar shahararrun adabin ƙasashen Sin da Laos a cibiyar baje-kolin kayayyakin duniya na Sin.
An fidda sakamakon fasara jere na farko na ayyukan fassara da Farfesa Lu Yunliang da mataimakiyar farfesa Li Xiaoyuan da malama Lu Huiling na kwalejin Asiya na jami’ar BFSU suka fasara.