JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

Shugaban BFSU ya halarci taron ilmin raya kimiyya na duniya

发布时间:2023-02-21

Daga ranar 13 zuwa ranar 14 ga watan Febrairu, an gudanar da taron ilmin raya kimiyya na duniya. Bisa goron gayyata da aka yi, an ce, shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamintin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar Yang Dan ya halarci taron. Shugaban kwalejin nazarin raya ilmi a kan Intanet kuma mataimakin shugaban kula da dakunan nazarin harsunan duniya da na AI Tang Jinlai ya halarci taron. Malaman da suka fito daga kwalejojin nazarin fasara da Turanci, da Faransanci, da Rashanci, da Larabci da harsunan Spaniya da na Portugal sun halarci taron, inda suka yi aikin tafinta da fassara abubuwa a taron.

Taken taron wannan karo shi ne “Gyare-gyare da aka samu ta kimiyya da makomar ilmi a nan gaba”, wakilan ƙasashe da yankunan sama da 130 sun halarci taron. A yayin bikin ƙaddamar da taron ministan ilmin Sin Huai Jinpeng ya shugabanci taron, mataimakiyar firaministar Sin Sun Chunlan ta yi jawabin fatan alheri, kuma firaministan New Zealand Chris Hipkins da mataimakin shugaban Philippines kuma ministan ilmin ƙasar Rodrigo Duterte da ministan kula da tattalin arziki da ilmi da imiyya na ƙasar Swiss Guy Parmelin da babban jami’ar dake kula da ƙungiyar ilmi da kimiyya da al’adun M.D.D. Audrey Azoulay, da mashawarcin musamman ga sakataren janar na M.D.D. game da taron ƙoli kan ilmi Leonardo Garnier sun yi fatan alheri ta hoton bidiyo.

A yayin taron, nagartattun malaman BFSU sun kafa rukunin aikin tafinta na harsunan Turanci da Faransanci da Rashanci da Larabci, da na Spaniya, kuma mahalartar taron gida da waje da ma’aikatar kula da ilmi sun jinjina ƙoƙarinsu na aikin tafinta, wanda ke bayar da babbar gudummawa ga shirya taron.



NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC