JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

An gudanar da taron ƙara wa juna sani na gamayyar nazarin ƙasashen duniya da shiyya-shiyya a BFSU

发布时间:2022-12-31

A ranar 18 ga watan Disambar shekarar 2022, an gudanar da taron ƙara wa juna sani na gamayyar nazarin ƙasashen duniya da shiyya-shiyya CCAS da jami’ar BFSU ta shirya ta hoton bidiyo, kuma taken taron shi ne “Samun dauwamammen ci gaba cikin moriyar juna”.

Gamayyar CCAS da ƙawacen jami’o’in harsunan waje na duniya GAFSU ya shirya, wanda ke ƙunshe da ƙwararru da masana da suka fito daga ƙasashe 181, kuma waɗanda ke nazarin harsuna sama da 100 a duniya.

Shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU kuma shugaban kwalejin nazarin shiyya-shiyya da ƙasashen duniya Yang Dan da tsohon dan majalisar dokokin Morocco kuma shugaban ƙungiyar sada zumunci tsakanin Morocco da Sin Muhammad Khalili da shugaban kwamintin nazarin fasara na ƙasar Sin Du Zhanyuan sun yi jawabin fatan alheri a yayin taron.

Shugaba Yang Dan ya yi muhimmin jawabi mai suna ma’anar zamanintar da ƙasar Sin ga ƙasashen duniya, sakatare janar na kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU kuma shugaban kwalejin nazarin ƙasashen duniya da shiyya-shiyya na Shanghai Jiang Feng ya yi muhimmin jawabi “Sabon nau’in wayewar kai ga samar da zaman lafiya da samun bunƙasuwa a ƙasashen duniya”. Farfesa a jami’ar UNED ta Costa Rica kuma tsohon mataimakin ministan tattalin arzikin ƙasar Velia Govaere da wakilin hukumar raya ilmi, kimiyya da al’adu ta UNESCO a kasar Mali Edmond Moukala sun yi jawabi ɗaya bayan ɗaya. Ƙwararru da masana sun yi sharhi da musanyar ra’ayi a yayin taron.

A yayin taron kuma, an gabatar da “Ilmin nazarin ƙasashe da shiyya-shiyya bisa duniyar da muke ciki”, kuma an fidda sabon littafin “lissafin duniya na 2022”.


NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC