JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

An ƙaddamar da taron koyar da Sinanci na ƙasa da ƙasa na 2022

发布时间:2022-12-14

A ranar 8 ga watan Disamba, aka ƙaddamar da taron koyar da Sinanci na ƙasa da ƙasa a birnin Beijing. Mataimakiyar firaministan Sin Sun Chunlan ta halarci bikin buɗe taron, inda ta yi muhimmin jawabi. Ministan kula da ilmin Sin Huai Jinpeng ya shugabanci taron. Shugaban jami’ar BFSU kuma mataimakin sakataren jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Yang Dan ya halarci bikin buɗe taron, inda ya shugabanci wani taron dake ƙarƙashin wannan babban taro, watau taron tattaunawa karo na farko na mu’amala da haɗin gwiwa game da harsunan gida da wajen ƙasar Sin.

Taken taron mu’amala da haɗin gwiwa game da harsunan gida da waje karo na farko shi ne, tuntuɓawa, mu’mala da fahimta, don kafa amincewar juna da haɗin gwiwa ta harsuna da al’adu. Cibiyar kula da mu’amala da haɗin gwiwa da harsunan gida da waje ta ma’aikatar ilmin Sin ta shirya wannan taro. BFSU da kamfanin ɗab’in littattafan koyar da harsunan waje da nazarinsu sun ɗauki nauyin shirya wannan taro. Direktan cibiyar kula da haɗin gwiwa da mu’amalar harsunan gida da waje Ma Jianfei da jakadan Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a ƙasar Sin Ali Al Dhaheri ya halarci bikin taron, inda ya yi jawabin fatan alheri. Shugabar kwalejin nazarin harsuna na Xu Guozhang kuma farfesa ta cibiyar nazarin harsunan waje da ilmin koyarwar Sin Wen Qiufang ta yi jawabi a yayin bikin buɗe taron. Kwararru da masana sama da ɗari da suka fito daga ƙasashe daban daban da wakilan hukumomin harsuna da al’adu sama da 10 na Sin sun halarci bikin.

A yayin taron tattaunawa, cibiyar kula da haɗin gwiwa da ma’amalar harsunan gida da waje ta gabatar da shiri, kwamintin kula da ilmi da al’adu na Birtaniya da sauran hukumomin harsunan ƙasa da ƙasa sama da 10 na duniya, sun gabatar da shirin haɗin gwiwa da mu’mala.



NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC