JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

An gudanar da taron ƙara wa juna sani kan littattafan koyarwa na harsunan waje karo na farko a Sin

发布时间:2022-11-30

Daga ranar 26 zuwa ranar 27 ga wata, an gudanar da taron ƙara wa juna sani game da littattafan koyarwa na harsunan waje karo na farko kuma taron share fagen kafa kwamintin kula da littattafan koyarwa na harsunan waje a ƙasar Sin. Taken taron shi ne nazarin littattafan koyarwa da harsunan waje bisa la’akari da duniya ke ciki da ƙirƙiro da sabbin tunani daga ƙasar Sin, ƙwararru da masana a wajen harsunan waje na ƙasar Sin kimanin dubu 10 sun halarci taron ta hoton bidiyo, inda suka tattauna hanyoyin da suke bi wajen nazarin littattafan koyarwa na harsunan waje a ƙarƙashin yanayin da ake ciki yanzu, don ƙara ba da gudummawa wajen bunƙasa sha’anin tsara littattafan koyarwa da ke da halayyen musamman na ƙasar Sin. Mataimakin hukumar kula da littattafan koyarwa na ma’aikatar kula da ilmin ƙasar Sin Chen Mao da babban sakataren jam’iyyar kwaminisanci ta jami’ar BFSU Wang Dinghua da shugaban kwamintin kula da nazarin kwatanta harsunan Sinanci da Turanci na ƙasar Sin Luo Xuanmin ya halarci bikin ƙaddamar da taron, inda zaunannen mamban kwamintin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU kuma mataimakin shugaban jami’ar Sun Youzhong ya shugabanci taron.

An kafa matakin muhimmin jawabi da taron ƙara wa juna sani da tarurruka cikin bambancin rukuni a yayin babban taron. Ƙwararru da masana na gida da wajen sun more fasahohinsu game da matakan da za a ɗauka wajen tsara littattafan koyarwa na harsunan waje da aka yi amfani da su a makarantun firamare, da sakandare, da jami’a har da kwalejoji da yadda za a nazari da amfani da tantance su, hatta ma da nazarin matakan da za a ɗauka wajen sanya al’adu a ciki, da nazarin littattafan harsunan waje na ƙasashen waje, da littattafan koyarwa da raya malamai a yayin taron.



NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC