JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

An gudanar da taron tattaunawar watsa labarun ƙasa da ƙasa game da al’adun ƙasar Sin a BFSU

发布时间:2022-11-18

A ranar 10 ga watan Nuwamban, cibiyar kula da yaɗa al’adu na hukumar kula da ɗab’i da harsunan ƙasashen waje da kwalejin nazarin yaɗa labarun ƙasa da ƙasa game da al’adun ƙasar Sin na BFSU da cibiyar nazarin wayewar kan ƙasar Sin ta kwalejin nazarin al’adun ƙasar Sin sun shirya taron tattaunar watsa labarun ƙasa da ƙasa game da al’adun ƙasar Sin a BFSU.

Mamban majalisar ba da shawara game da harkokin siyasa karo na 13 na  ƙasar Sin kuma mataimakin shugaban kwamintin kabilu da addini Jiang Jianguo da mataimakin shugaban kwalejin nazarin al’adun ƙasar Sin Ji Lin, da direktan hukumar kula da ɗab’i da harsunan waje Du Zhanyuan, da mataimakin babban sakataren jam’iyyar kwaminisancin BFSU kuma shugaban BFSU Yang Dan, da mataimakin sakataren jam’iyyar kwaminisancin kwalejin nazarin faɗar sarki kuma mataimakin shugaban kwalejin Luo Xianliang, da sakatare janar na haɗaɗɗen kwamintin nazarin Confucius na ƙasa da ƙasa Jia Deyong sun halarci biki tare da gabatar da jawabi, inda baƙi na gida da waje kimanin 100 sun yi mu’amala sosai. Babban sakataren jam’iyyar kwaminisancin BFSU Wang Dinghua ya yi shawarwari da baƙi kafin aka ƙaddamar da taron. Mataimakin shugaban hukumar kula da ɗab’i da harsunan waje Lu Caihong ya shugabanci bikin ƙaddamar da taron, inda zaunannen mamban jam’iyyar kwaminisancin BFSU kuma mataimakin BFSU Zhao Gang ya shugabanci taron gabatar da jawabi.

Taken taron shi ne “Yaɗa labaru a ƙasa da ƙasa game da wayewar kan ƙasar Sin a ƙarƙashin sabon yanayin da ake ciki”, inda aka gayyaci ƙwararru da masana a fannin yaɗa labarun ƙasa da ƙasa game da al’adun ƙasar Sin a gida da waje, kuma masanin ƙasar Sin da suka fito daga ƙasashen Rasha da Afirka, da Latin Amurka sun halarci bikin, inda suka ƙoƙarta wajen lalubo yanayin da ake ciki wajen nazarin al’adun ƙasar Sin da ma’anarta a duniya, da ƙirƙiro da sabbin tunani, don gina gamayyar ɗan Adam don yin shawarwari game da wayewar kai. A ƙarƙashin taron tattaunawa, akwai “Koyi wayewar kai da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen gida da waje” da “Raya al’adu da yaɗa labaru” da nazarin masana’antun ƙetaren ƙasashe da nazarin al’adun ƙasar Sin” da “Masani matasa da yada al’adun ƙasar Sin”, don tattauna hanyoyin da za a bi wajen yaɗa al’adun ƙasar Sin.


NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC