JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

An kafa gamayyar haɗin gwiwa kan nazarin ƙasashe da shiyyoyi ta Sin a BFSU

发布时间:2022-11-04

A ranar 23 ga watan Oktoban shekarar 2022, an kafa gamayyar haɗin gwiwa kan nazarin ƙasashe da shiyyoyi ta ƙasar Sin a BFSU. Fannin karatu na nazarin ƙasashe da shiyyoyi ya zama wani fannin karatu da da aka kafa. Don inganta wannan fannin, da kafa tsarin fannonin karatu da ilmi da maganganu na nazarin ƙasashe da shiyyoyi da ke da halayye musamman na ƙasar Sin , da lalubo bakin zaren hanyoyin horar da ɗalibai da inganta ba da hidimmomi ga ƙasar Sin da zamantakewar al’umma da kafa gamayyar ɗan Adam, BFSU ta gabatar da shawarar kafa wannan gamayya.

Mataimakin ministan sashen kula da tuntuɓawar jam’iyyun ƙasashen waje na kwamintin tsakiya na jam’iyyar kwaminisancin ƙasar Sin Yu Hongjun da tsohon shugaban jami’ar Renmin Liu Wei, da mataimakin direktan sashen kula da zamantakewar al’umma da kimiyya na ma’aikatar ilmin ƙasar Sin Tan Fangzheng, da mataimakin direktan sashen kula da mu’amala da tuntuɓawar ƙasashen waje na ma’aikatar ilmin Sin Jia Peng, da sakataren jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dinghua da mataimakin sakatare kuma shugaban jami’ar Yang Dan, da mataimakin sakatare kuma mataimakin jami’ar Jia Wenjian, da zaunannen mamban jam’iyyar kwaminisancin jami’ar kuma mataimakin shugaban jami’ar Zhao Gang sun halarci taron. Shugabanni da masana na jami’o’i sama da 30 da suka fito daga jami’ar Peking, da Tsinhua, da Fudan, UIBE, da CUPL da dai sauransu sun halarci taron.

A gun taron tattaunawar da aka shirya, mataimakin shugaban jami’ar Jia Wenjian ya shugabanci taron. Shugabanni mahalartar taron da masana da kwararru sun gabatar da jawabi ɗaya bayan ɗaya, inda suka yi mu’amala game da ra’ayoyinsu game da raya waɗannan fannonin karatu. Shugaban jami’ar Yang Dan ya yi babban jawabi mai take “Tinkarar ƙalubalen da ake fuskanta da gamayya.”



NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC