JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

Malaman BFSU sun kammala ayyukan nazari na asusun kula da kimiyya da zamantakewar al’ummar ƙasar Sin cikin cikakkiyar nasara

发布时间:2022-10-19

A shekarar 2022, ofishin kula da tsare-tsaren nazarin kimiyya da zamantakewar al’umma da ra’ayin fahimtar duniya watau falsafa na Sin ya bayar, an ce, an kammala ayyuka da yawa da malaman BFSU suka shirya cikin cikakkiyar nasara, kuma bayan da aka tantance su, sun zama fitattun ayyuka. A ciki, akwai aikin nazari kan tantance ma’aunin koyarwa ɗalibai masu neman digiri na farko na fannonin karatu na harsunan waje a jami’o’in Sin da zaunannen mamban jam’iyyar kwaminisancin BFSU kuma mataimakin BFSU Sun Youzhong ya ɗauka, haka kuma akwai aikin nazari kan bambancin harsunan Turanci da Sinanci game da lokaci da wurare da ma alaƙar da ke tsakaninsu wajen koyon harshen da ba harshen uwa ba da aikin nazarin dangantakar adabin Sin da ƙasar Poland da mataimakiyar farfesa na harshen Polish na kwalejin nazarin harsuna da al’adu na Turai Li Yinan ta ɗauka, kuma an tantance dukkansu don su zaman na fitattun ayyuka. Ya zuwa yanzu, yawan fitattun ayyuka da BFSU ta ɗauka ya kai kashi 37.5 cikin 100.


NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC