JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

An ƙaddamar da taron tattaunawar shugabannin kwalejojin Confucius na 2022

发布时间:2022-09-20

A ranar 14 ga watan Satumban shekarar 2022, an ƙaddamar da taron tattaunawar shugabannin kwalejojin Confucius na 2022 da asusun kula da ilmin koyar da Sinanci na duniya na Sin da jami’ar BFSU suka shirya, kuma ofishin kula da ɗab’in littattafan harsunan waje da nazari suka shirya. Mataimakin shugaban asusun kula da koyar da Sinanci na duniya a ƙasar Sin kuma sakatare janar Zhao Lingshan, kuma shugaban BFSU da mataimakin sakataren janar Yang Dan da mataimakin sakataren jam’iyyar kwaminisancin jami’ar kuma mataimakin shugaban BFSU Jia Wenjian sun halarci bikin. Mataimakin sakataren asusun Yu Yunfeng ya shugabanci wannan biki.

An ƙaddamar da taron don inganta haɗin gwiwa tsakanin kwalejojin Confucius, da yalwata bunƙasuwa, don lalubo bakin zaren samun bunƙasuwa cikin dogon lokaci. Za a yi taron zuwa ranar 24 ga wata, don tattauna matakan da za a ɗauka wajen kyautata yanayin malamai, da yin mu’amala da more fasahohi wajen samun bunƙasuwa. Za a gayyaci farfesa Roger T. Ames na jami’ar Hawaii ta Amurka don more fahimtarsa game da ra’ayin Confucius na Sin.

A matsayin ɗaya daga cikin ayyukan tuna da ranar Confucius ta duniya, za a shirya jawabai 2 da tarurrukan tattaunawa 3, shugabannin kwalejojin Sin 600 sun yi rajistar shiga cikin wannan aiki, kuma shugabannin Confucius 26 za su gabatar da jawabi.


NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC