A ranar 18 ga watan Yuli, an ƙaddamar da bikin buɗe kwas koyon ilmin Confucius da al’adun ƙasar Sin, da jami’ar BFSU da haɗaɗɗen kwamintin koyon ilmin Confucius na ƙasa da ƙasa suka shirya. Mataimakin shugaban haɗaɗɗen kwamintin koyon ilmin Confucius Zhang Xuezhi da zaunannen mamban kuma mataimakin shugaban jami’ar koyon harsunan waje Zhao Gang sun halarci taron. Kwararren kwalejin nazarin yaɗa al’adun Sin a ƙasashen duniya na BFSU kuma mataimakin shugaban haɗaɗɗen kwamintin nazarin ilmin Confucius na ƙasa da ƙasa kuma mai nazarin ra’ayin sanin duniya An Lezhe da ɗalibai sun halarci wannan kwas.
An shafe kwanaki 13 ana gudanar da kwas da harshen Sinanci da Turanci a kan Intanet, ɗalibai kimanin 160 da suka fito daga ƙasashen Moroco, da Pakistan, da Swiss, da Sin, da Masar, da Indiya, da Birtaniya, da Ireland, da Uruguay, da Afghanistan, da Austriya, da Rasha, da Argentina, da Azerbaijan, da Venezuela, da Amurka, da Lithuania, da Iran, da Albaniya, da Kazakhstan, da Ecuador, da Peru, da Brazil, da Turkiya, watau ƙasashe da yankuna 24 sun halarci kwas.