JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

An ƙaddamar da taron tattaunawa karo na 10 kan aikin fassara na Asiya da tekun Fasific a BFSU

发布时间:2022-07-13

A ranar 25 ga watan Yuni, BFSU ta ɗauki nauyin shirya taron tattaunawa karo na 10 kan aikin fassara na Asiya da tekun Fasific da ƙawacen masu aikin fassara na duniya da kwamintin fassara na Sin suka shirya tare.

Shugaban kwamintin fasara na ƙasar Sin kuma shugaban hukumar kula da dab’in mujalloli da harsunan waje, Du Zhanyuan, da shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren jam’iyyar kwaminisancin BFSU Yang Dan, da shugaban ƙawacen masu aikin fassara na duniya Alison Rodrigue, da shugaban kwamintin haɗin gwiwa na kwalejin aikin fassara na ƙasa da ƙasa Bart Defrancq sun halarci bikin ƙaddamar da taro gami da bayar da jawabi. Taken taron shi ne “Haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen duniya wajen aikin fassara: sabon hali, sabon yanayi da sabon salo. Wakilan masu aikin fassara 300 da suka fito daga ƙasashe da yankuna 35 sun halarci taro a kan Intanet da kuma a jami’ar BFSU.


NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC