JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

An fidda sabbabin fitattun fannonin karatu na BFSU

发布时间:2022-06-22

Kwanan baya, ma’aikatar kula da ilmin ƙasar Sin ta fidda jerin sunayen sabbabin fitattun fannonin karatu na shekarar 2021 na ƙasar Sin da na birnin Beijing, Fannonin karatu na haɗa-haɗar kudi, harsunan Hausa, da Swaihili, da Hindi, da Sanskrit-Pali da Latina, da harsunan ƙasashen Indonesiya, da Vietnam, da Slovakiya, da Serbiya, da Girka, da Bangladesh, da Netherlands, da Finland, da Ukraine, da na Danmark, da Norway, da kimiyya da fasahar Kwamfuta, da nazari da daidaita harkokin sadarwa, da tafiyar da harkokin masana’antu da kasuwanci, da daidaita harkokin kasuwanci ta fasahohin zamani sun zama fannonin karatu da ƙasar Sin za ta sanya ƙarfi wajen gina su. Yayin da harsunan Amharic, da Zulu, da Pilipino, da Urdu, da Mongol, da Hebrew, da harsunan ƙasashen Nepal, da Armeniya, da Croatian, da Iceland sun zama manyan fannonin karatu da za a tashi tsaye don gina su a birnin Beijing. BFSU ta samu fitattun fannonin karatu 54 da ƙasar Sin za ta ƙoƙarta wajen gina su, yayin da ta samu fannonin karatu 18 da za a raya su.


NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC