Bisa labarin da shafin Internat na gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing ta bayar a ranar 10 ga wata, a rana ta farko bayan da aka kammala bikin sabuwar shekara ta Sinawa, an buga waya ga Gao Xiaofan, bayan da ta gama da aiki, ƙarfe 6 ya yi. A wannan rana, watau ranar haihuwarta, a matsayinta na mai aikin sa kai na jami’ar BFSU, ta ɗauki nauyin karɓar tawagar Ukraine ta gasar wasannin Olympics. Ta kasance ɗaya daga cikin masu aikin sa kai sama da 900 daga jami’ar BFSU a gasar wasannin Olympics na wannan karo.
Che Jiayi da Zou Guanglin su ma masu aikin sa kai na tawagar Amurka da ta Japan su bayyana cewa, kowa na girmamar juna, kuma suna son wannan yanayin aiki. Ana wasa tare da kallon gasar tare da warware matsalolin dake fuskanta. Ana zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya.
Wannan ba ma kawai ya zama wata damar aiki ga masu aikin sa kai ba, har ma ta kyautata halayyensu. Ko da yake bai kai wata guda ba da ko wane mai aikin sa kai ya shiga cikin wannan aiki, amma kowa ya samu ɗaukaka sosai. Tawagogin wasanni da suka karɓa, su zama malamai da abokansu.
A ranar 31 ga watan Janairu, watau bikin sabuwar shekara ta Sinawa, masu aikin sa kai suna wuraren aiki a maimakon haɗuwar da mambobin iyali. Yayin da ake cikin mota zuwa ɗakunan wasanni, ’yan wasannin Ice Hockey su bayyana wa wata mai aikin sa kai Che Jiayi cewa, abin baƙin ciki da ba ki iya haɗuwa tare da iyali ba, amma su yi imani cewa, za su yi alfahari da su.
A ranar 4 ga watan Fabrairu na shekarar 2022, da ƙarfe takwas na dare, yayin da aka fara bikin buɗe gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing a hukunce, ba a samu ko wane mai aikin sa kai a wajen kujerun ’yan kallo ba. Kowa yana shan aiki wajen jagorancin tawagogi don shiga cikin filayen wasanni, wannan ya zama wani muhimmin aiki. Zou Guanglin ya ƙara da cewa, muna ganewa idanunmu wannan tarihi, har ma mu zama wani bangare daga cikinsu.