JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

An kaddamar da taron tattaunawa karo na biyu kan sha’anin koyarwa na kasa da kasa na BFSU

发布时间:2021-11-11

A ranar 23 ga wata, an kaddamar da taron shekara-shekara na kwamintin sashen koyarwar kasa da kasa na kwamintin koyarwar kasar Sin kuma taron tattaunawa karo na biyu kan sha’anin koyarwa na kasa da kasa da kwatanta sha’anin koyarwa na shekarar 2021 na BFSU.

Sakatare janar na kwamintin hukumar kula da ilmi da kimiyya da al’adun M.D.D na kasar Sin Qin Changsheng da shugaban kwamintin kula da sashen koyarwar kasa da kasa na kwamintin koyarwar Sin kuma babban sakataren jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dinghua ya halarci taron.

Wang Dinghua ya yi babban jawabi mai take “Inganta kwarewar kasar Sin wajen daidaita batun koyarwar kasar Sin.” Ya bayyana cewa, za a inganta kwarewar kasar Sin wajen shiga cikin sha’anin koyarwa a duniya. Ya kamata a mai da hankali game da inganta sha’anin horar da kwararru, da kara nazari kan sha’anin koyarwa na duniya, da kara yada labaru game da yadda kasar Sin ta kyautata sha’anin koyarwa, da inganta mu’amala da hadin gwiwa da kasashen duniya, da kafa dandalin koyarwa na kasa da kasa da kasashen duniya.

A gun bikin kaddamar da taron, an gudanar da bikin mika lambobin yabo na kirkiro da sabbin tunani game da sha’anin koyarwa na yankin Asiya da tekun Fasific. Shirye-shirye na “Hoton bidiyo: Kada a daina karatu a lokacin barkewar cutar numfashi ta Covid-19” na kwalejin koyarwar Maldives, da shirye-shirye “Inganta sha’anin koyarwa ta kimiyya da fasaha don yaki da cutar Covid-19” na asusun Himalaya na kasar Nepal sun samu lambobin yabo na Wenhui.


NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC