A yammacin ranar 21 ga watan Satumba, an kaddamar da bikin fara koyar da sabon fannin karat una Amharic a kwalejin nazarin Afrika na jami’ar BFSU. Zaunannen mamban kwamitin tsakiya kuma mataimakin shugaban jami’ar BFSU Jia Wenjian da minista kuma karamin jakadan na ofishin jakadancin kasar Habasha da ke kasar Sin Samuel Fitsumbirhan ya halarci bikin, kuma shugabar kwalejin nazarin Afrika Li Hongfeng ta shugabanci bikin.