Daga ranar 16 zuwa ranar 25 ga watan Disamba na shekarar 2019, bisa goron gayyata da jami’ar Zayed ta Hadaddiyar Daular Larabawa da cibiyar nazari da mu’amalar ilmi ta Saudiyya da cibiyar mu’amalar ilmi Nabig ta Saudiyya da gwamnatin Amman ta Jordan da kungiyar kula da biranen kasashen Larabawa suka yi, babban sakataren jami’ar BFSU Wang Dinghua ya shugabanci tawaga don ziyartar kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa, Saudiyya da Jordan, inda aka cimma kwalliya ta biya kudin sabulu.