JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

BFSU ta samu lambar yabon fitacciyar hukumar hadin gwiwa karo na biyar daga babban taron ilmin Sinanci na kasa da kasa

发布时间:2019-12-28

Daga ranar 9 zuwa ranar 10 ga watan Disamba, an yi babban taro game da koyar da ilmin Sinanci na kasa da kasa na shekarar 2019 a birnin Changsha da ke kasar Sin. Mataimakiyar firaministan Sin kuma shugabar kwamintin cibiyar kwalejin Confucius Sun Chunlan ta halarci bikin bude taron, inda ta yi muhimmin jawabi. Ministan ilmi na Sin kuma mataimakin shugaban kwamintin cibiyar kwalejin Confucius Chen Baosheng ya shugabanci taron.

Taken taro na wannan karo shi ne kirkiro da sabbin abubuwa da raya ilmin Sinanci na kasa da kasa a zamanin yanzu, an shirya dandalin tattaunawa guda da sauran kananan tarurrukan kara wa juna sani 32, aka yi mu’amala da tattaunawa game da batutuwa na hada Sinanci da sana’o’i, da tsara manufofi da ka’idoji da zaben malamai da littattafai da hanyoyin koyarwa da jarrabawa da kyautata ayyuka da karfafa hadin gwiwar kasashen duniya game da koyar da ilmin Sinanci a kasashen duniya. Wakilan hukumomin koyar da Sinanci da kwalejojin Confucius sama da 1000 na kasashe da yankunan sama da 160 sun halarci taron. Zaunannen mamban kwamintin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma mataimakin shugaban BFSU Yan Guohua ya halarci taron.


NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC