JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

Shugaban majalisar dokokin Czech ya ziyarci BFSU

发布时间:2019-11-30

A ranar 7 ga watan Nuwamba na safe, shugaban majalisar dokokin kasar Czech Radek Vondráček ya shugabanci tawaga don ziyartar jami’ar BFSU gami da yin jawabi. Jakadan kasar Czech da ke kasar Sin Vladimir Tomsik da direktar kwamitin tattalin arziki na majalisar dokokin kasar Radim Fiala da mataimakiyar ministan harkokin kasuwanci da cinikayya ta kasar Martina Taubelova sun ziyarci jami’ar tare. Shugaban jami’ar Yang Dan ya yi shawarwari da tawaga, kuma ya halarci bikin jawabi. Mataimakin shugaban jami’ar Yan Guohua ya jagoranci bikin jawabi.

A madadin jami’ar BFSU da sakataren jami’ar Wang Dinghua, shugaban jami’ar Yang Dan ya yi lale marhabin da zuwa shugaban majalisar Vondráček. A cikin jawabi nasa, Ya waiwayi tarihin mu’amala tsakanin kasashen Sin da Czech, musamaman ma game da gudummawar da tsoffin malamai suka bayar wajen koyarwa da nazarin harshen Czech a kasar Sin. Yang Dan ya yi nuni da cewa, shekarar 2019 zagayowar shekara ta 70 wajen kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen Sin da Czech, kuma shekara ta 65 game da kafuwar sashen harshen Czech a jami’ar BFSU. A cikin dogon lokaci, gwamnatin Czech da ofishin jakadancin Czech da ke Sin sun ba da cikakken goyon baya ga jami’ar. Bangarorin biyu suna fatan ci gaba da hadin gwiwa kafada da kafada don kawo makoma mai haske game da nazarin al’adun Bohemistika a kasar Sin da raya dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Vondráček ya yi jawabi game da rawar da Czech ta taka a yankin tsakiyar Turai da kungiyar EU. Ya yi nuni da cewa, jamhuriyar Czech ta yi fici wajen masana’antu, kuma yayin da take bin dokokin kungiyar EU, kuma ta gudanar da manufar cinikayya ta bude kofa ga kasashen waje. Sin tana sahon gaba wajen raya ababen more rayuwa, kuma shigar da Czech cikin shirin Ziri Daya da Hanya Daya yana da amfani ga tattalin arzikin kasar, Sin ta kasance babbar abokiyar cinikayya ta kasar Czech a nahiyar Asiya, Czech tana fatan ci gaba da karfafa hadin gwiwa da kasar Sin, don inganta fahimtar juna da dankon zumunci a tsakanin jama’ar kasashen biyu. A lokacin da Vondráček ya amsa tambayoyin da dalibai suka bayar, ya amsa tambayoyi game da sha’awar Czech don shiga yankin da ke yin amfani da kudin Euro, da tasirin da batun janyen jiki na Birtaniya daga kungiyar EU zai haifar ga Czech da makomar dangantakar kasashen biyu.

Kafin aka yi jawabi, dalibai masu koyon harshen Czech sun gabatar da wasanni raye-raye na Mazurke ga baki, kuma sun rera shahararriyar wakar Czech, wanda ya samu karbuwa daga baki.


NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC