北京外国语大学亚洲学院揭牌仪式配图.jpg
北京外国语大学非洲学院揭牌仪式配图.jpg
A ranar 23 ga watan Satumba, an gudanar da bikin kafa kwalejin nazarin Asiya da kwalejin nazarin Afrika a jami’ar BFSU.
Babban sakatare na kwamitin jam’iyyar kwaminis ta jami’ar BFSU Wang Dinghua, da shugaban tawagar jakadun kasashen Afrika a kasar Sin kuma jakadan Kamaru a kasar Sin Martin Mpana da jakadan kasar Morocco a kasar Sin Aziz Mekouar da jakadan kasar Nepal a kasar Sin Leela Mani Paudyal da jakadan kasar Bangladesh dake kasar Sin M Fazlul Karim, da ministar kasar Afrika ta Kudu a kasar Sin Madam Debora Balatseng da karamin jakadan kasar Malaysia dake kasar Sin a fannin ilmi Hou Chunxing da sauran jami’an diflomasiyya na kasashe 15 na Asiya da Afrika sama da 20, da sauran tsoffin jakadun kasar Sin a kasashen waje sama da 20, sakatare na cibiyar hadin gwiwar Sin da kasashen Asean Chen Dehai da direktan dake kula da batun Afrika na ma’aikatar harkokin waje na kasar Sin Dai Bing da direktan kula da jami’o’i na ma’aikatar ilmi ta Sin Wu Yan da ma sauran shugabanni da kwararru na sauran jami’o’I 25, da shugabannin jami’ar BFSU dake birnin Beijing, da wakilan malamai da dalibai sama da 1000 sun halarci bikin.
Wang Dinghua da Wu Yan da Chen Dehai da Leela Mani Paudyal da Hou Chunxing da M Fazlul Karim da shugabar kwalejin nazarin Asiya Su Yingying sun cire kyallaye na kwalejin Asiya. Wang Dinghua da Daibing da Aziz Mekouar da tsohon jakadan Sin a kasashen Gabon da Kamaru kuma abokin karat una jami’ar Xue Jinwei, da Madam Debora Balatseng da shugabar kwalejin nazarin Afrika Li Hongfeng sun cire kyallaye ga kwalejin.