A safiyar ranar 27 ga watan Yuni, an shirya bikin kammala karatun digiri na farko na shekarar 2019 kuma bikin mika digiri a dakin wasan motsa jiki na jami’ar. Dalibai masu neman digiri na farko na gida da waje kimanin 1428 sun halarci bikin, kuma 62 daga cikinsu sun samu lambobin yabo na nagartattun daliban birnin Beijing, yayin da sauran karin 110 sun zama nagartattun daliban BFSU, sauran dalibai 87 sun zama mambobin kwamintin dake kula da abokan karatu na BFSU.