JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

Ministan ilmi na Hadaddiyar Daular Larabawa ya ziyarci BFSU

发布时间:2019-06-30

A yammacin ranar 20 ga watan Yuni, ministan ilmi na Hadaddiyar Daular Larabawa Hussain Al Hammadi ya shugabanci tawaga don kai ziyara a jami’ar BFSU. Babban sakatare na jami’ar BFSU Wang Dinghua da mamban zaunannen kwaminti na jam’iyyar kwaminisancin BFSU kuma mataimakin shugaban BFSU Yan Guohua sun gana da ministan.

Babban sakatare Wang ya yi maraba da zuwan tawagar a jami’ar BFSU, kuma ya jinjina goyon baya da taimako da sarakunan Hadaddiyar Daular Larabawa da gwamnatin suka bayar ga kwalejin Larabawa na BFSU. Ya gabatar da halin da jami’o’in Sin suke ciki da tarihin BFSU da gine-ginen fannonin karatu da horar da dalibai da sauran batutuwa, musamman ma ya waiwayi baya game da ci gaban da kwalejin Larabawa da cibiyar nazarin Larabci da addinin Musulunci ta Zayed suka samu, yana fatan ma’aikatar ilmi ta kasar za ta nuna goyon baya ga inganta hadin gwiwa tsakanin jami’ar BFSU da ma sauran cibiyoyin nazarin kasar, don gina laburaren Zayed, kuma ya gayyaci ministan Hussain don ya sake ziyartar BFSU a badi, don murnar zagayowar shekaru 80 da kafa BFSU.

Hussain ya gode wa karbuwa da jami’ar BFSU ta shirya masa, ya waiwayi ci gaban da kasashen Sin da Hadaddiyar Daular Larabawa suka samu wajen hadin gwiwar ilmi, ya jinjina gudummawar da kwalejin Larabawa ya samu wajen inganta hadin gwiwar sada zumunta a tsakanin kasashen biyu kuma ma’aikatarsa tana fatan nuna goyon baya da kawo sauki ga raya jami’ar BFSU, kuma yana fatan kara mu’amala a tsakaninsu game da koyar da Sinanci da nazarin kasashe da shiyya-shiyya da nazarin fasahohin zamani don yalwata hakikanin hadin gwiwa tsakanin jami’o’i da cibiyoyin nazari na kasashen biyu.

Mataimakin shugaban Yan Guohua ya yi maraba da zuwan Hussain a jami’ar, ya bayyana takaitaccen bayani na kwalejin Zayed da BFSU ta shirya, kuma ya gayyaci Hussain don ya ziyarci kwalejin, da kara nuna masa goyon baya.

 

NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC