JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

Yawan harsunan waje da BFSU take shirya koyarwa ya kai 101

发布时间:2019-05-15

Kwanan baya, ma’aikatar kula da harkokin ilmi ta kasar Sin ta fidda sakamakon da take amincewa game da sabbin fannonin karatun digiri na farko da za a bude a kasar na shekarar 2018, inda ta amince da fannonin karatu guda 6 da BFSU ta gabatar, wadanda suka hada da harsunan Tamazight da Jawa da Punjabi, da fannin karatun nazarin harsunan waje da tarihin waje, da ilmin yada labaru, da nazarin kungiyoyin kasa da kasa da daidaita batutuwan duniya.

Ke nan, yawan fannonin karatun digiri na farko da BFSU take shirya koyarwa ya karu zuwa 121, cikinsu aka hada da fannonin karatu na harsunan waje 102, da sauran fannoni da ba na harsunan waje ba guda 19. Fannonin karatu guda 45 sun kasance fannonin karatu kacal da ake koyarwa a kasar Sin.

NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC