JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

Mataimakin ministan ilmin Siriya ya ziyarci BFSU

发布时间:2019-05-15

A ranar 25 ga watan Nuwanba, sakatare janar na jami’ar BFSU Wang Dinghua ya gana da mataimakin ministan ilmin kasar Siriya Farah Sulaiman Al.Mutlak.

Wang Dinghua ya yi maraba da zuwa Al.Mutlak, kuma ya gabatar da tarihin jami’ar da fiffikon koyarwa da bunkasuwar sashen Larabci a jami’ar, kasashen Sin da Siriya na da dankon zumunci a cikin tarihi, kuma yana fata za su kara inganta hadin gwiwa game da jami’ar BFSU da sauran jami’o’in kasar Siriya game da nazarin ilmi da koyar da Larabci.

A nasa bangare kuma, Al. Mutlak ya bayyana cewa, akwai malaman koyar da Larabci da yawa a kasar Siriya, akwai makoma mai haske wajen inganta hadin gwiwa a tsakaninsu. A sa’i daya kuma, ya yi farin ciki da BFSU ta gayyace shi don halartar taron tattaunawa karo na biyu da ke karkashin taken “Ziri daya da hanya daya”, kuma yana sa ran zai tattauna da masu harkokin ilmi na kasashen da ke Ziri daya da hanya daya, don inganta fahimtar juna da cude-ni-in-cude-ka a tsakaninsu.

Taron tattaunawa kasa da kasa kan ilmi na kasashen Ziri daya da hanya daya, wani muhimmin taron tattauna da aka shirya tsakanin masu harkokin ilmi na wadannan kasashe, jami’ar BFSU ta dauki nauyin shirya wani kashi na taro kan ilmi da zamani da raya kasa. Akwai kwararru da masana sama da 50 da suka fito daga kasashe 9 za su tattauna da musayar ra’ayi game da “Kwadago da raya tattalin arziki da samun bunkasuwa” “Bambancin al’adu a cikin ilmin kasashen duniya” “Dunkulewar kasashen duniya bai daya da zamanintar da al’umma” da “Nazari da kirkiro da sabbin abubuwa, da samun bunkasuwa cikin dogon lokaci.”

NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC