A ranar 11 ga watan Afrilu,aka kaddamar da jerin bukukkuwa don tunawa cikon shekaru 100 da haihuwar shugaban Hadaddiyar daular Larabawa Zayed a kwalejin nazarin harshen Larabci na BFSU. Shugaban BFSU Peng Long da taimakinsa Yan Guohua, da jakadan Hadaddiyar Daular Larabawa Ali Zahiri da sauran jakadun kasashen Larabawa sama da 10 da malamai da daliban kwalejin, da wakilan hukumomin gwamnati da na kafofin yada labaru har da na masana’antu kimanin 300 sun halarci bikin.Shugaban cibiyar nazarin Larabci da addinin Musulunci ta Zayed na BFSU Furfesa Xue Qingguo ya shugabanci taron.