An yi rajistar kafa asusun tarbiya na BFSU a ranar 18 ga watan Nuwamban shekarar 2010, dalilin da ya sa aka kafa asusun shi ne don amsa gudunmawa don yaba wa koyarwa da karatu da sa kaimi ga raya jami’ar. Asusun ya karbi gudunmawa daga kungiyoyin sa kai da masana’antu da jama’a. Za a yi amfani da dukiyoyin asusun don raya tarbiyar BFSU, da kyautata yanayin karatu, da yabawa nagartattun malamai da dalibai, don ba da tallafi ga nazari da koyarwa da dab’I, har ma da taimakawa dalibai don su shiga cikin ayyukan kasa da kasa, da tallafawa malamai don su yi karatu a kasashen waje da halartar taron nazarin kasa da kasa da taron hadin gwiwa . Game da ba da kudin gudunmawan musamman, za a yi amfani da kudaden da masu bayarwa suke son.
Asusun yana sa ran samun goyon baya da taimako daga masana’antun gida da waje da kungiyoyi da jama’a na sana’o’I daban daban.
Hanyoyin tuntubawa:
Waya: 0086-10-88810271 0086-10-88817794
Naurar aika takardu: 0086-10-88810192
E-mail: jjh@bfsu.edu.cn
Shafin yanar gizo: jjh.bfsu.edu.cn
Adireshi: 51D, 501A、501B Hawa na 5 na ginin sashen Larabci dake gabashin jami’ar BFSU (No 2 na arewacin zoben hanya na uku a yankin Haidian dake birnin Beijing)